ABNA24: Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa an fara shimfada bututun iskar gas din ne daga tsibin Kish da ke kudu maso gabacin tekun Farisa a cikin kasar, zuwa inda za’a hada shi da babban bututun iskar gas na kasa mai lamba 7 da ke kimani kilomita 94 daga tsibirin.
Labarin ya kara da cewa kamfanin NIOC karkashin kamfanin man fetur na kasar ne zai gudanar da aikin a cikin kwanaki 20 masu zuwa.
Za’a shimfida bututu mai fadin inci 32 karkashin ruwan tekun farisa mai zurfi ne, har zuwa inda za’a hau da shi kan tudu.
Ana saran kasar Iran za ta fidda iskar gas kimani cubic mita biliyon daya a shekara ta 2021 mai zuwa. Sannan kasar ce ta hudu a duniya, bayan kasashen Amurka, Rasha fa kuma Sin a yawan fidda iskar gas.
342/